Gwamnan Jihar Kano Abba Kabir Yusuf ya umarci masarautun Kano huɗu da suka haɗa da Kano da Karaye da Gaya da Rano su shirya gudanar da bikin Hawan Ƙaramar Sallah.
Gwamnan ne ya bayyana haka a wata sanarwa da mai magana da yawunsa Sunusi Bature Dawakin Tofa, ya fitar a ranar Talata.
Gwamnan ya bayyana cewa ba za su lamunci maƙiya su hana jama’ar jihar ‘yancinsu na gudanar da hawan Sallah ba.
Ya kuma tabbatar da cewa jami’an tsaro za su bayar da kariya ga jama’a.