Rundunar yan sandan Rivers ta musanta labarin kai hari gidan tsohon gwamnan jihar kuma ministan birnin tarayya Abuja Nyesom Wike, da aka ce an ƙone ƙurmus.
Rundunar ta sanar da hakan cikin wata sanarwa da kakakin ta SP Grace Iringe-Koko, ta fitar sannan tace an yada labarin da manufar kawo hargitsi a jihar Rivers.
Sanarwar tace ko kadan babu gaskiya a cikin labarin data ayyana a matsayin wanda aka fitar don saka fargaba a zukatan al’ummar Rivers masu bin doka da ka’ida.
Rundunar ta kuma ce babu wani abun daya faru a Rivers mai kama da zanga-zanga ko ƙone ƙone.