Shugaban kasa Tinubu ya gana da manyan hafsoshin tsaron kasa, da babban sifeton yan sanda da kuma shugabannin majalisun dokin kasa.
:::Wike ya kwace filin sakatariyar jam’iyyar PDP dake Abuja
Duk da cewa ba’a bayyana dalilin gudanar da ganawar ba, amma hakan yazo yan awanni bayan da wasu bama-bamai suka tarwatsa daya daga cikin bututun man fetur a jihar Rivers mai fama da rikicin siyasa.
An fara ganawar da misalin karfe 3 na rana a fadar shugaban dake birnin tarayya Abuja.
Wadanda suka halarci taron sun hadar da shugaban majalisar dattawa Godswill Akpabio, kakakin majalisar wakilai Tajuddeen Abbas da mataimakin sa Benjamin Kalu.
Sai dai babu wata cikakkiyar sanarwar dake nuni da cewa shugabannin majalisar sun shiga ganawar Tinubu da manyan hafsoshin tsaron.
Daga fannin tsaro kuwa an ga fuskar mai bawa Tinubu shawara a fannin tsaro Nuhu Ribadu, shugaban DSS Adeola Ajayi, da shugaban hukumar leken asiri ta kasa NIA Mohammed Mohammed.
Although the reason for the emergency conclave is unclear, it comes just hours after an explosion rocked a section of the Trans Niger Pipeline in Bodo Community in Gonna Local Government Area of Rivers State.
The explosion occurred late on Monday night near the Bodo-Bonny Road under construction.