Majalisar wakilai ta amince da kudirin dokar harajin da shugaban Kasa Tinubu ya aike mata.
Majalisar ta amince da kudirin dokar a yau Talata, bayan shugaban kasar ya aike mata kudirin a watan Oktoba na shekarar 2024.
A zaman majalisar na ranar Alhamis, data gabata ne majalisar ta yi nazari tare da amincewa da rahoton Kwamitin Kudi, wanda ya yi aiki a kan kudirorin dake cikin dokar bayan yin nazari akan shawarwarin da ‘yan Najeriya suka bayar dangane da kudirin.
Idan za’a iya tunawa kudirin dokar harajin ya haifar da cece-kuce musamman a tsakanin mutanen arewa da suka bayyana cewa akwai cutarwa a kunshe cikin kudirin dokar harajin.