Farashin litar man fetur yakai naira 8000 a jamhuriyar Nijar

0
136

Jaridar Sunday Punch, ta rawaito cewa ana cigaba da fuskantar matsanancin karancin man fetur a jamhuriyar Nijar mai makwabtaka da Nijeriya, a daidai lokacin da hukumar hana fasa kwauri ta Najeriya tace zata cigaba da aiwatar da dokar hana fasa kwaurin fetur zuwa Nijar.

Idan za’a iya tunawa an rufe gidajen man fetur na yan kasuwar Najeriya guda 400 dake iyakar Najeriya da Nijar tun a shekarar 2019, lokacin da ake kokarin sanin aininhin man fetur din da yan Nijeriya ke amfani da shi.

:::https://dailynews24ng.com/hausa/2025/03/18/yan-majalisar-wakilai-2-sun-fice-daga-pdp-zuwa-apc/

A ranar litinin data gabata hukumar hana fasa kauri ta Najeriya tace gidajen man zasu cigaba da kasancewa a rufe, kamar yadda mai magana da yawun hukumar Abdullahi Maiwada, ya sanar.

Punch, ta kara da cewa tsadar fetur da ake cigaba da fuskanta a jamhuriyar Nijar zai sanya a rika yin kokarin safarar man daga Najeriya zuwa Nijar don samun kazamar riba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here