Atiku ya ƙalubalanci Tinubu akan dokar ta ɓacin jihar Rivers

0
26

Ɗan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP a zaɓen shekarar 2023 Atiku Abubakar, ya ƙalubalanci shugaban ƙasa Tinubu akan yadda ya saka dokar ta ɓaci a jihar Rivers.

Tinubu ya cutar da al’ummar Rivers wajen ƙaƙaba musu dokar, inji Atiku Abubakar

Atiku Abubakar, yace Tinubu ya gaza ɗaukar matakan da suka dace wajen magance rikicin siyasar Rivers.

Cikin wata sanarwar daya fitar a yammacin ranar Talata Atiku, yace sanya dokar zai haifar da rashin jituwa tsakanin magoya bayan APC da PDP a Rivers.

Idan za’a iya tunawa shugaba Tinubu ya sanya dokar ta ɓaci a Rivers tare da dakatar da gwamnan jihar Siminalaya Fubara da mataimakiyar sa, haɗi da mambobin majalisar dokokin jihar tsawon watanni 6, sakamakon rikicin siyasar da yaƙi ci yaƙi cinyewa.

Tinubu ya kuma naɗa Vice Admiral Ibok Ibas, mai ritaya a matsayin gwamnan Rivers na riƙo.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here