Tsohon ɗan takarar gwamna na jam’iyyar PDP na Jihar Legas, Dr Abdul-Azeez Adediran, ya fice daga jam’iyyar PDP zuwa jam’iyyar APC.
Adeniran ya sanar da hakan a yau Litinin yayin wani taron manema labarai daya gudanar a ofishinsa da ke Ikeja, a Legas, makonni kaɗan bayan yin murabus din sa daga PDP.
Ya bayyana cewa kafin yanke shawarar komawa APC, ya tattauna da abokan siyasa, magoya baya, da shugabanni daga jam’iyyu daban-daban, ciki har da SDP, ADC, da YPP, sannan ya yanke wannan hukunci.