Sojojin Najeriya dake karkashin bataliya ta uku sun samu nasarar kama wasu manyan yan ta’addan da suka addabi al’ummar arewa ta tsakiya.
Shalkwatar tsaron ƙasa ce ta tabbatar da hakan cikin wata sanarwa data fitar.
Sanarwar tace jami’an tsaro sun dade suna neman yan ta’addan amma sai yanzu aka samu damar kama su.
WaÉ—anda aka kama sun haÉ—a da Bashir Mohammed da Ismail Mohammad, da aka kama a jihar Filato tare da makamai bayan samun wani bayanan sirri daga jami’an tsaro.