Tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo, ya bayyana takaicin sa akan yadda yace sarautar gargajiya tana cigaba rasa martabar ta a Najeriya.
Obasanjo, ya bayyana hakan a cikin sabon littafin sa mai suna “Nigeria Past and Future”
Ya kuma bayyana cewa akwai masu laifi, ’yan daba, da masu safarar miyagun ƙwayoyi da suka zama sarakuna a wasu yankunan Najeriya, inda yace wannan abu ne mai matuƙar ban takaici, kuma yana daga cikin matsalolin da ke addabar Najeriya.
Ya ce dole ne a dawo da mutunci da kimar sarautar gargajiya domin tana taka rawar gani a ci gaban ƙasa.
Har ila yau, ya gargaɗi shugabanni cewa idan ba su magance matsalolin da jama’a ke fuskanta ba, hakan na iya haifar da rikici a nan gaba.