Majalisar dokokin jihar Rivers ta miƙa takardar zargi akan gwamna Fubara da mataimakiyar sa.
Majalisar Dokokin Jihar Rivers ta mika wata takarda mai alaka da zargin aikata rashin da’a ga Gwamna Siminalayi Fubara da mataimakiyarsa, Ngozi Odu.
Matakin dai wani yunkuri ne na tsige Gwamnan da Mataimakiyar sa daga ‘yan majalisar dake goyan bayan Ministan Abuja Nyesome Wike.