Rundunar Hisbah ta jihar Kano ta kama Rukayya Ibrahim, wadda aka fi sani da Ummin Mama ba maiyi sai Allah, wadda ta kware wajen yada badala a shafin ta na TikTok.
Daily News 24 Hausa, ta rawaito cewa Mataimakin babban kwamandan rundunar Dr Mujahiddin Aminudden Abubakar, ne ya sanar da hakan a yau, yana mai cewa wadda suka kama bata da aiki sai yada batsa da tsiraicin ta, wanda hakan babban laifi ne a addinin muslinci.
A lokacin da ake zantawa da ita Ummin Mama, ta tabbatar da cewa tana yin bidiyon batsa don ta samu mabiya a shafin ta na TikTok wato (followers) amma tace yanzu bata yi wasu ne ke daukar bidiyon nata suna yin amfani dashi a shafin su domin suma su samu mabiya.
Ta kuma ce iyayen ta sun hana ta yin wannan mummunan hali, amma ta bijire musu, tare da cewa wanda zai aure ta ma yayi kokarin hana ta yin batsa a TikTok.
Kamar yadda ta sanar da bakin ta Ummin Mama, tace ita yar unguwar Me Dileli, Shagari QTRS ce, wadda aka kama ta a gidan Zoo.
Dr. Mujahiddin Aminudden Abubakar, yace rundunar Hisbah zata gurfanar da ita bayan kammala bincike.