Gwamnatin Kano ta kafa kwamitin da zai kawo karshen yankewa ma’aikata albashi

0
96

Gwmanatin Kano ta kaddamar da kwamitin da zai rika bayyana albashin ma’aikata don gujewa yankan albashin da aka samu wasu suna yi.

Gwamnatin tace kwamitin zai rika yin aikin bayyana adadin albashin ma’aikatan da za’a biya kafin turawa kowanne ma’aikaci kudi.

Sakataren gwamnatin Kano Umar Farouk Ibrahim, ne ya kaddamar da kwamitin a yau Litinin.

Gwamnatin ta umarci dukkan ma’aikatan jihar da su gabatar da kawunansu domin tantancesu gabanin biyansu albashin watan Maris.

Yace za’a tantance ma’aikatan saboda korafin da suka yi lokacin biyan su albashin watan Fabrairu.

Idan za’a iya tunawa a kwanakin baya ne gwamnan jihar Kano ya dauki matakin kora akan wasu ma’aikatan da aka samu da hada baki wajen yankewa ma’aikata albashi da kuma kin biyan wasu ma’aikatan baki daya.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here