Gwamnatin Kaduna ta rage kuɗin rijistar makarantun gaba da sakandire

0
50

Gwamnatin jihar Kaduna ta sanar da rage yawan kudin rijistar dalibai a makarantun gaba da sakandire mallakin jihar.

Bayanin hakan na cikin wata sanarwa da gwamnatin jihar ta fitar, tana mai cewa Gwamna Uba Sani, ne ya amince a rage kuɗin, don saukakawa dalibai da iyaye.

Sanarwar tace an rage kudin rajistar jami’ar Kaduna (KASU) daga Naira 150,000 zuwa Naira 105,000 sai  kwalejin Nuhu Bamalli da aka rage kuɗin rijistar daga Naira 100,000 zuwa Naira 50,000.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here