Dan gidan Gwamnan Jihar Bauchi Shamsudeen Bala Mohammed ya ja hankalin dan gidan Shugaban Kasa Seyi Tinubu akan yawon da yake yi jihohin Arewa yana raba abinci.
Shamsudddeen yace masa, don Allah Seyi Tinubu idan lokacin zuwan ka Bauchi yayi bama bukatar shinkafa a leda, kazo ka bawa Matasan mu tallafin aiki na da sana’a kamar Keke Napep, kudaden da zasu yi kasuwanci, ka dauki nauyin koya musu kimiyyar sadarwa ICT, da daukar nauyin koya musu kasuwancin Crypto
Shamsudddeen yace matasan Bauchi basa bukatar abinci da shinkafar da ake rabawa a leda, sai dai a dauki nauyin koya musu sana’a bawai basu abincin da zasu ci a lokaci daya ba, saboda su ba mabarata bane.