Wata Mai aikin hidimtawa kasa ta ankarar da al’umma akan yadda take fuskantar sakonni na barazana, bayan ta wallafa bidiyon da take kalubalantar manufofin gwamnatiin Tinubu, akan tsadar rayuwa da matsalolin tattalin arziki.
Matashiyar ta kasance mai hidimar kasa a jihar Lagos, mahaifar shugaban kasar.
Mai bautar kasar ta wallafa kalubalen tattalin arzikin a shafin ta na TikTok mai suna @talktoraye, kuma faifan bidiyon ya zagaya sosai a shafukan sada zumunta.
Ta fito karara ta caccaki shugaban kasa Bola Tinubu, inda ta kira shi da sunan “mugun shugaba,” kuma ta yi tambaya kan irin matakan da gwamnati ke dauka na rage wa ‘yan kasa radadin talauci.
Tace tsarin NYSC bashi da wani amfani a wajen ta, saboda tana kashe kudin daya zarce abinda ake bata a matsayin alawus a kowanne wata.
Bayan haka tace tana karɓar sakonni na barazana daga jami’an hukumar NYSC.
Zuwa yanzu hukumar ta NYSC bata ce komai dangane da zargin ba.