Dr. Sani Ibrahim Sani Kaita, na Jami’ar Ahmadu Bello Zariya, ya bayyana shirin da gwamnatin jihar Katsina ta samar na farfado da kiwon dabbobi a tsakanin mata da matasa a matsayin tsarin da zai inganta tattalin arziki, da bunkasar sa.
Idan za’a iya tunawa a kwanakin baya ne gwamnan jihar Katsina Dikko Umar Radda, ya kaddamar da rabon Akuyoyi ga masu karamin karfi dake rayuwa a daukacin kananun hukumomin jihar.
Dr. Kaita, ya kasance sakataren gudanarwa a sashin ilimi na Jami’ar Ahmadu Bello Zariya, wanda cikin wata sanarwa daya fitar yayi bayanin cewa rabon dabbobin ga mabukatan cikin al’umma zai habbaka dogaro da kai da kuma samun wadatuwar kudi a hannun mutane.
Wannan shirin ba wai kawai zai samar da guraben aikin yi ga mata da matasa ba, zai kuma taimaka wajen kawar da munanan dabi’un da suka addabi al’ummar mu da dadewa, in ji Dr. Kaita