Zanga-zanga ta barke a jihar Rivers yayin da matasa suka banka wutar a gidan ministan Abuja Nyesom Wike.
Majiyar jaridar Dailyexcessive, ta rawaito cewa matasan sun ƙone motocin dake gidan tare da sauran wasu kayayyaki.
Majiyar tace matasan sun yi haka da manufar hana tsohon gwamnan jihar kuma ministan Abuja Nyesom Wike, dawowa Rivers, akan zargin sa da cin amanar mahaifiyar sa, dangane da rikicin siyasar dake tsakanin sa da gwamna Fubara.
Jaridar tace zuwa yanzu an jibge jami’an tsaro a gidan don daidaita al’amura da kwantar da hankalin al’umma.