Yar majalisar dattawa mai wakiltar Jihar Kogi ta tsakiya Natasha Akpoti, tace tana sane da shirin kama ta da jami’an tsaron Najeriya keyi da zarar ta shigo kasar.
Natasha ta sanar da hakan a yau Lahadi yayin da take zantawa da manema labarai a kasar Amurka.
Natasha taje birnin New York, na Amurka inda ta kaiwa majalisar dinkin duniya korafi dangane da zargin take mata hakki a majalisar dokokin kasa karkashin jagorancin Akpabio, da take zargin sa da neman yin lalata da ita.
Natasha tace tabbas akwai shirin kama ta in har ta sauka a birnin tarayya Abuja.
Sanatar da aka dakatar ta kara da cewa shugaban majalisar dattawa ya tura wasu jami’an diflomasiyyar Najeriya dake Amurka don su fitar da ita daga zauren majalisar dinkin duniya bayan kai koken ta, inda tace jami’an wasu kasashe sun kubutar da ita tare da taimakon jami’an tsaro.
Zuwa wannan lokaci ba’a samu damar jin ta bakin shugaban majalisar dattawa Sanata Akpabio akan zargin Natasha ba.