Mahukuntan Amurka sun kama wata malamar makarantar sakandaren dake yankin California da ake zargi da lalata da wani ɗalibi mai shekaru 17.
Wannan da ba shi ne karon farko da aka tuhumi wani da irin wannan laifi a makaranatar ba.
A cewar jami’an ’yan sandan Riverbank an kama malama Dulce Flores, mai shekara 28 bayan da ta kulla dangantakar da ba ta dace ba da wani dalibi dan shekara 17 a makarantar sakandare ta Riberbank a 2023.
Malamar wacce take koyar da harshen Sipaniya tana aiki a makarantar tun 2016.
Wata sanarwa da ‘yan sandan suka fitar ta ce, an fara gudanar da binciken bayan wani jami’in makarantar ya samu labarin alakar malamar da dalibin.
Zuwa yanzu an rufe malamar a gidan yari, yayin da ake sa ran bayar da belin ta akan dala 20,000.