Akwai alamun dake bayyana cewa wasu tsaffin ministocin gwmanatin tsohon shugaban Kasa Buhari na shirin ficewa daga APC zuwa jam’iyyar SDP.
Daya daga cikin yan majalisar Dokoki ta tara, wanda ya yi magana da jaridar PUNCH bisa sirri, ya ce aƙalla tsofaffin ministoci 10 daga gwamnatin Buhari na shirin komawa SDP.
Majiyar tace mutanen suna shirin kammala tattaunawa da jam’iyyar SDP a matakin jihohin su kafin shiga jam’iyyar.
Punch ta rawaito cewa manyan magoya bayan Buhari a wannan sauyi sun haɗar da tsohon Shugaban Jam’iyyar APC na Kasa, Abdullahi Adamu, tsohon Ministan Shari’a, Abubakar Malami, da kuma tsohon Shugaban Majalisar Dattawa, Ahmed Lawan.