Yan ta’addan da suka sace gwarzon Musabaƙar Al-Qur’ani ta kasa Abdulsalam Rabi’u, a jihar Katsina sun nemi Naira miliyan 30 a matsayin kuɗin fansa.
Gwamnatin jihar Katsina ta tabbatar da cewa gwarzon musabaƙar da mahaifin sa wanda akayi garkuwa dasu tare suna nan cikin koshin lafiya a hannun masu garkuwar.
Bayanin hakan na cikin wata sanarwa da kwamishinan yada labarai da al’adu na Katsina Dr. Bala Salisu ya fitar a ranar Juma’a.
Idan za’a iya tunawa kwanaki biyu da suka shude aka sace Abdulsalam Rabi’u, a hanyar sa ta zuwa Faskari daga Katsina bayan gwamnan jihar Dikko Radda, ya karrama shi tare da bashi mota.
Kafin fitar sanarwar ta gwamnatin Katsina an fara yada labaran cewa masu garkuwar sun hallaka Abdulsalam Rabi’u.
Sai dai gwamnatin ta ce masu garkuwar basu kashe shi ba, amma sun nemi a basu Naira miliyan 30 kudin fansa kafin sakin hafizin, duk da cewa kwamishinan yace zasu yi duk mai yiwuwa wajen kubutar da mahaddacin.