An kama malamin da ya kashe Almajirin sa dan shekara 14 a Jigawa.
Rundunar yan sandan jihar ce ta kama Malam Musa Wada mai shekaru 45, bisa zargin kisan dalibin nasa mai suna Bashir Adamu.
Daily News 24 ta rawaito cewa kakakin rundunar yan sandan jihar SP Lawan Shiisu, yace wanda ake zargin ya bayyana cewa shine yayi kisan ta hanyar yiwa Almajirin dukan da ya sanya har ya fita daga hayyacin sa, daga baya kuma ya rasu, saboda bai zo makaranta akan lokaci ba.
An samu malamin ya cire tsiraicin dalibin nasa bayan ya mutu, inda ake zargin yayi hakan da manufar yin tsafi da sassan mamacin.