Gwamnatin Kano tace Kotu bata cire Sarki Sunusi daga sarauta ba

0
72

Gwamnatin jihar Kano tace Kotun Daukaka Kara ba ta rushe nadin da ta yiwa Sarkin Kano na 16 Muhammadu Sunusi II ba.

Kwamishinan shari‘a na jihar Haruna Isa Dederi ne ya fadi haka yayin da yake jawabi kan hukuncin kotun na ranar Juma‘a.

Yace kotun daukaka kara ba ta rushe hukuncin da ta yi a baya ba, sai dai ya ce jama’a su saurara har zuwa lokacin da Kotun Kolin zata yi hukunci akan shari’ar masarautar.

Idan za’a iya tunawa a ranar juma’ar data gabata ne aka bayyana cewa kotun daukaka karar tace a dakatar da hukuncin daya bayar da damar naÉ—in da gwamnatin Kano ta yiwa Sarkin Kano Muhammadu Sunusi II.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here