Tsohon gwamnan jihar Kaduna Malam Nasir El-Rufa’i, yace bai taɓa zagin dattawan arewa ba.
Yace a lokacin daya bayyana hakan da yan siyasa yake magana bawai dattawan arewa ba.
Ya kara da cewa mutanen da suke kiran kansu da sunan dattawan arewa kansu kawai suka sani, saboda a cewar sa basu cika aikata gaskiya ba, saboda yayi aiki dasu.
Tsohon gwamnan na Kaduna ya bayyana hakan a lokacin da yayi wata ganawa da BBC Hausa.
El-Rufa’i yace yana fatan nan gaba kadan Peter Obi da Atiku Abubakar, Rotimi Ameachi, Rauf Aregbesola da duk wasu yan adawa su biyo shi cikin jam’iyyar SDP don kwace mulki daga hannun APC.
A bangare guda yace suna sane da irin matsalolin Tinubu amma suka amince ya yi mulki Najeriya, saboda sun ga ya gyara Lagos, tare da zaton zai iya gyara kasar nan, sai dai ya kasa yin abun daya dace.