Tinubu yace shugabannin baya sun gaza yiwa wadanda za’a haifa tanadi

0
59
Bola Ahmed Tinubu
Bola Ahmed Tinubu

Shugaban kasa, Bola Tinubu ya ce sauye-sauyen tattalin arziki da gwamnatinsa take yi, hakan nufin gyara makomar yara masu tasowa ne.

Yayin da yake jawabi ga ƙungiyar ƴan majalisa ta uku wadda ya kasance cikin ta a Jamhuriya ta uku lokacin da suka kai masa ziyara, Shugaba Tinubu ya ce a baya ƙasar na kashe kuɗaɗen yan Najeriya da ba a kai ga haihuwarsa ba.

Yace Shekara 50 da suka gabata, Najeriya na kashe kuɗaɗen yaran da ba a kai ga haihuwarsu ba, tare da mayar da hankali kan man fetur wajen samun kuɗin shiga. 

Shugaban ya kuma bayyana tarin matsalolin da ya fuskanta a farkon mulkinsa, musamman fannin tattalin arzikin da rayuwar jama’a.

Tinubu ya kara da cewa matakan daya dauka a farkon mulkin sa sune suka hana Najeriya lalacewa, saboda a cewar sa ya tarar da tarin matsaloli.

Sai dai a yanzu ya ce an fara ganin amfanin manufofin gwamnatiin sa.

Bayan haka yace farashin abinci yayi kasa sannan canjin kudaden ketare ya daidaita.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here