Gwamnatin tarayya ta musanta zargin Amurka akan kashe Kristocin Najeriya 

0
84

Amurka tace ana fakewa da rashin tsaro wajen farmakar Kristocin Najeriya, da kashe su.

Sai dai gwamnatin tarayya ta hannun ma’aikatar harkokin waje ta musanta zargin.

Wani rahoton ma’aikatar harkokin waje ta Amurka yayi zargin cewa ana kaiwa Kristoci hari, da kuma kawo rikicin addini a Najeriya.

Rahoton yace akwai yiwuwar Amurka ta sanyawa kasar nan takunkumi dangane da hakan.

Kimiebi Ebienfa, wanda shine mai magana da yawun ma’aikatar harkokin waje ta kasa ya fitar da sanarwar cewa zargin bashi da tushe ballantana makama.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here