Gwamnan Rivers zai sake gabatar da kasafin kudin jihar ga majalisa

0
47

Gwmanan jihar Rivers Siminalaya Fubara, rubuta wasika zuwa ga shugaban majalisar dokokin jihar Martin Amaewhule, don bashi damar sake gabatar musu da kasafin kudin shekarar 2025.

Fubara ya rubuta wasikar mai dauke da kwanan watan 13 ga watan Maris, inda ya nemi su bashi lokacin gabatar da zai bayyana kasafin kudin a duk lokacin da yayi musu daidai.

A cikin wasikar Fubara yace jami’an tsaro sun hana shi damar shiga zauren majalisar dokokin a ranar larabar data gabata lokacin da ya taho da tawagar sa da nufin gabatar da kasafin, duk da cewa ya sanar da shugaban majalisar shirin sa na zuwa.

Gwamnan na Rivers ya kara da cewa yaje majalisar domin yin biyayya ga hukuncin kotun koli akan sake gabatarwa majalisa kasafin.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here