Baffa Bichi da Diggol sun ziyarci Barau Maliya

0
59

Tsohon sakataren gwamnatin jihar Kano Abdullahi Baffa Bichi da tsohon kwamishinan sufuri na Kano Muhammad Gambo Diggol sun ziyarci mataimakin shugaban majalisar Dattawa Barau I Jibril, a gidan sa dake birnin tarayya Abuja, a yau juma’a.

Barau I Jibril, ya bayyana jin dadin sa akan ziyarar da manyan yan siyasar na jihar Kano suka kai masa.

Idan za’a iya tunawa dai a kwanakin baya ne gwamnan jihar Kano Abba Kabir Yusuf, ya sauke mutanen biyu daga mukaman su, lokacin da ya yiwa majalisar zartarwar Kano garambawul.

Zuwa yanzu dai ba’a bayyana dalilin ziyarar ba da kuma abin da suka tattauna.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here