Kotun daukaka kara tace har yanzu Sarkin Kano na 15 Alhaji Aminu Ado Bayero, shine cikakken Sarkin Kano.
Kotun ta kuma ce har yanzu Sarakuna 5 ne a jihar Kano.
Kotun Wadda Tayi hukuncin Yau juma’a kuma ta dakatar da hukuncin mayar da Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II, kan karagar sarautar Kano a wannan lokaci
Matakin ya biyo bayan daukaka kara da aka yi, yayin da ake jiran hukuncin Kotun Koli kan rikicin masarautar.
A kwanakin baya wata Kotun Daukaka kara dake birnin tarayya Abuja ta yanke hukuncin cewa babbar kotun Tarayya bata da hurumin sauraron Shari’ar Masarautar kano.