Kwamared Waiya ya cancanci mukamin kwamishina a Kano—Kungiyar Matasan Arewa

0
91

Kungiyar matasan arewacin Najeriya ta bayyana jin dadin ta akan yadda Gwmanan jihar Kano Abba Kabir Yusuf, ya basa Kwamared Ibrahim Abdullahi Waiya, mukamin kwamishinan yada labarai da al’amuran cikin gida. 

Gamayyar kungiyoyin matasan arewa sama da 100, tace naɗin Waiya a matsayin kwamishina abun alfahari ne wanda ba za’a yi dana sani ba.

Bayanin hakan na cikin wata sanarwa da Kwamared Aliyu Mohammed, ya fitar.

Matasan sun ce suna da tabbacin Waiya zai yi amfani da kwarewar da yake da ita wadda zata kawo cigaba a fannin da aka bashi mukami da jihar Kano baki daya, sannan zai taka rawa a majalisar zartarwar Kano a fannin shugabanci, gaskiya da sanya al’umma a harkokin gwamnati.

Daga karshe kungiyar tayi fatan samun nasara ga Kwamared Waiya a shugabancin sa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here