Rundunar yan sandan kasa reshen birnin tarayya Abuja, ta sanar da samun nasarar kashe fitaccen dan bindiga mai garkuwa da mutane Dogo Saleh, wanda ya addabi wasu yankunan birnin, kamar yadda kakakin rundunar SP Josephine Adeh, tace Dogo, ya takurawa mutanen wasu sassan Abuja da rashin zaman lafiya musamman garkuwa da mutane domin karbar kudin fansa.
SP Josephine Adeh, tace kisan dan bindigar ya biyo bayan samun bayanan sirrin da yan sanda suka samu tare da kai hari maboyar sa domin kama shi.
Adeh tace harbe-harben da aka samu tsakanin yan sanda da tawagar Dogo Saleh, ne ya kai ga kisan nasa.
Rundunar yan sandan Abuja ta kara da cewa wanda ta kashe din shine ya addabi hanyar Abuja zuwa Kaduna don tare mutane da sace su. Rahotanni sun nuna cewa an kubutar da wasu mutanen da yayi garkuwa dasu a yayin harin da suka kai.