Kwamitin zartarwa na PDP ya shiga  ganawar sirri

0
71

Kwamitin gudanar da ayyukan cikin gida na jam’iyyar PDP a matakin kasa ya shiga wata ganawa mai muhimmanci.

Punch ta rawaito cewa ana gudanar da taron a sakatariyar jam’iyyar PDP dake birnin tarayya Abuja a cikin sirri.

Shugaban PDP na kasa Umar Damagum, shine ke jagorantar zaman na yau, wanda shine taro na farko da shugabannin suka yi tun bayan hukuncin kotun koli akan rikicin mukamin sakataren jam’iyyar tsakanin Senator Samuel Anyanwu da Sunday Udeh-Okoye.

Kawo yanzu ba’a samu cikakken bayani akan dalilin shirya taron ba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here