An samu rikici a gaban majalisar dokokin jihar Rivers a lokacin da jami’an tsaro suka hana gwamnan jihar Rivers Siminalaya Fubara, yayi niyyar shiga majalisar don gabatar da kasafin kudin shekarar 2025.
Jami’an tsaron majalisar sun sanar da Fubara cewa sun rufe kofar shiga majalisar saboda basu da masaniya akan ziyarar gwamnan.
Amman Fubara ya bayyana musu cewa kafin zuwan nasa sai da ya sanar da kakakin majalisar dokokin Amaewhule, cewa zai zo don gabatar musu da kasafin kudin, kamar yadda jaridar Nigerianbulletin ta rawaito.
Rahotanni sun tabbatar da cewa a dole Fubara ya koma gidan gwamnati ba tare da samun damar shiga cikin majalisar ba.
Sai dai anyi zargin kakakin majalisar dokokin Amaewhule, da cewa shi ya hana jami’an tsaro bawa Gwamnan damar shiga majalisar saboda tankiyar dake tsakanin su.
Shi dai Amaewhule, ya kasance mai goyon bayan ministan birnin tarayya Abuja Nyesom Wike, wanda ke takun saka da Siminalaya Fubara.