Inuwa Waya da AA Zaura sun kalubalanci jam’iyyar APC

0
32

Tsohon dan takarar gwamnan jihar Kano a jam’iyyar APC Alhaji Inuwa Waya, ya ziyarci tsohon dan takarar Sanatan Kano ta tsakiya Alhaji Abdussalam Abdulkarim AA. Zaura, a gidan sa dake birnin tarayya Abuja.

Bayanin hakan na cikin wata sanarwa da Daraktan hulda da kafafen sadarwa na AA Zaura, Sulaiman Amir Rangaza ya fitar.

Sanarwar tace yan siyasar sun tattauna akan makomar siyasar su da matsayin su a cikin APC.

Sanarwar tayi zargin cewa shugabancin jam’iyyar APC yayi watsi da yan siyasar biyu duk da irin gudunmuwar da suka bayar a yayin zaÉ“en shekarar 2023, da kuma taimakawa yan jam’iyyar. Amma a yanzu ba’a damawa dasu a kowanne al’amari na jam’iyyar.

Inuwa Waya da AA Zaura, sun nemi APC ta rika mutunta daukacin yayanta da kuma kokarin hada kai don samun nasara da inganta Najeriya.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here