Gwamnan Borno ya rabawa kananun yan kasuwa naira biliyan 1

0
46

Gwamnan Jihar Borno, Babagana Umara Zulum, ya raba wa ƙananan ’yan kasuwa da matsakaita mutum 9,403 a ƙananan hukumomin Biu da Hawul, tallafin Naira biliyan ɗaya.

An bayar da tallafin don ƙarfafa kasuwanci, haɓaka tattalin arziƙi, da rage talauci a kananun hukumomin.

A Biu da Hawul, gwamnan ya raba Naira miliyan 560.3 ga ’yan kasuwa 5,603, inda kowane mutum ya samu Naira 100,000.

Hakazalika, ya raba Naira miliyan 439.7 ga matasa da magidanta 1,800 a Biu da kuma ’yan kasuwa 2,000 a Hawul.

Gwamna Zulum ya ce gwamnatinsa za ta ci gaba da tallafa wa ƙananan ’yan kasuwa da matasa don bunƙasa tattalin arziƙi da samar da ayyukan yi.

Ya buƙaci waɗanda suka samu tallafin da su yi amfani da shi yadda ya kamata, inda ya bayyana cewa hakan na daga cikin alƙawuran da ya ɗauka a lokacin yaƙin neman zaɓe.

Har ila yau, ya umarci hukumar zuba jari ta Jihar Borno (BOSIMP) da ta tantance ƙarin matasa 2,000 marasa galihu domin su ma su amfana da tallafin a nan gaba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here