Ƴan bindiga sun sace gwarzon Musabaƙar Al-Qur’ani ta kasa da aka gudanar a jihar Kebbi Abdussalam Rabi’u Zakari, da mahaifin sa a jihar Katsina.
Rahotanni sun bayyana cewa lamarin ya faru a hanyarsu ta dawowa daga Katsina zuwa garin Faskari, bayan da gwamnan jihar Dikko Umar Radda, ya karrama Abdulsalam.
Ƴan bindigar sun tare su a kusa da labin Bangori, kan hanyar Funtua zuwa Gusau.
Daya daga cikin yan uwan mahaddacin mai suna Sagir Rabi’u, yace mutanen suna cikin motar da aka bawa Abdulsalam, lokacin da ya lashe gasar Musabaƙar.
Ya kara da cewa abin takaicin shine da azumi a bakin su yayin da wannan mummunan abu ya afku akan su.