Wasu jihohin Najeriya zasu fuskanci tsananin zafin rana

0
81

Hukumar hasashen yanayi ta kasa NIMET, tace akwai yiwuwar samun tsanantar zafi a wasu daga cikin jihohin Najeriya har na tsawon kwanaki hudu.

NIMET, tace hakan zai sanya mutane fuskantar sauyawar al’amuran su na yau da kullum a tsakanin ranakun da za’a samu karuwar zafin ranar.

Jihohin da aka yi hasashen za su fuskanci zafin sune Neja, Kwara, Oyo, Kogi, Nasarawa da Benue.

Sai Kuma Enugu, Anambra, Abia, Ebonyi, Cross River da birnin tarayya Abuja, Taraba, Adamawa, Plateau, Kaduna, Zamfara da Sokoto.

Bayanin hakan na cikin wata sanarwa da hukumar ta fitar a jiya Litinin.

NIMET, ta shawarci al’umma dasu kiyaye shiga cikin rana daga karfe 12 zuwa 3 na rana don gujewa fuskantar matsala daga zafin.

Ta kuma shawarci al’umma da su riÆ™a shan isasshen ruwa su kuma yi amfani da fanka da na’urar sanyaya É—aki da kuma zama a wurare masu inuwa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here