Tinubu ya nemi gwamnoni da ministoci su tallafawa mabukata

0
55

Shugaban kasa Bola Tinubu, ya nemi gwamnoni da ministocin sa su rika kyautatawa mabukata ta hanyar fito da tsare tsaren da zasu tallafi marasa karfi.

Tinubu ya bayyana hakan a daren Litinin lokacin da ya shiryawa gwamnonin da ministoci liyafar cin abincin buÉ—a baki na Azumin Ramadan a fadar sa dake birnin tarayya Abuja.

Shugabannin hukumomin gwamnatin tarayya suma sun samu gayyatar cin abincin tare da shugaba Tinubu.

Shugaban ya kuma roki a dena yin shugabancin nuna son rai, sannan ya nemi gwamnoni su zamo ginshikin kai Najeriya tudun mun tsira.

Tinubu, yace zuwa yanzu an fara ganin amfanin manufofin sa, yana mai cewa akwai bukatar goya masa baya don samun nasara a kokarin da yake yi na garambawul ga tattalin arzikin kasar nan.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here