Jami’an sojin kasar nan sun samu nasarar hallaka yan ta’addan da suka addabi jihar Zamfara su 37, lokacin da sojin suka gudanar da wani atisayen hadin gwuiwa da dakarun fansan Yamma.
Kwararren mai wallafa bayanai da suka shafi al’amuran tsaro a yankin Tafkin Chadi, Zagazola Makama, ya bayyana cewa an gabatar da harin da manufar fatattakar yan ta’adda daga maboyarsu ta karamar hukumar Kaura Namoda a Zamfara.
:::Cutar sankarau ta hallaka mutane da yawa a Najeriya
Majiyar Zagazola Makama, tace an kaddamar da harin da yayi sanadiyyar mutuwar mayakan a ranar 10 ga watan Maris da muke ciki.
An bayyana cewa harin jirgin saman da sojin suka kaddamar da misalin karfe 11:00 na safe a jiya Litinin, ya sanya an samu gagarumar nasara akan yan bindigar. Sannan wasu mayakan sun tsere zuwa cikin daji bayan anyi musu munannan rauni tare da cewa ana bibiyar wadanda suka tsere don kama su.