Karin cajin ATM zai hana masu karamin karfi yin ma’amala da bankuna—Majalisa

0
13

Majalisar wakilai ta umarci babban bankin kasa CBN ya dakatar da karin kudin da aka yiwa masu ma’amala da bankuna in sun cire kudi daga na’urar ATM.

Majalisar ta kuma bayyana damuwar ta akan cewa karin cajin ATM zai hana masu karamin karfi yin ma’amala da bankuna, wanda hakan ya sabawa muradun babban bankin na CBN.

:::Bafarawa ya musanta komawa jam’iyyar SDP

Majalisar wakilan ta kuma bayyana cewa kafin karin harajin na ATM, tun tuni yan Najeriya ke fama da maban-bantan karin haraji da tsadar rayuwa da kuma hauhawar farashin kayan masarufi bayan tsadar man fetur da karin kudin wutar lantarki, wanda hakan ya saka kunci a zukatan yan kasa.

Bukatar hakan tazo a daidai lokacin da dan majalisa Marcus Onobun, ya gabatar da kudirin neman dakatar da karin harajin.

Marcus Onobun, yace sabon cajin da CBN ya bijiro dashi ya sanya ana daukar naira 100, da karin naira 500, idan mutane sun ciri kudi daga ATM, ko a manyan shagunan yin siyayya.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here