Tsohon gwamnan jihar Kaduna Malam Nasir El-Rufa’i, yace Gwamnatin APC ce ta jefa jam’iyyun LP, PDP da NNPP a cikin rikici.
The Guardian ta bayyana cewa El-Rufai ya yi wannan zargi lokacin da ya ke jawabi ga wasu mambobin jam’iyyar SDP, bayan ya koma cikin ta a jiya litinin.
Ya kuma bayyana cewa akwai mutanen da aka dauka aiki domin haddasa rikici a jam’iyyun adawar kasar nan don rage musu tasiri.
Malam El-Rufa’i, yace gwamnatin APC ce ta haddasa rikicin jam’iyyar LP, sannan itace tayi haka a PDP da NNPP. Inda ya kara da cewa akwai mutanen da suke karÉ“ar albashi don kawo rikici a cikin NNPP.
El-Rufa’i, yace rikicin jam’iyyun adawar da ake yi a kotuna duk APC ce ta haddasa shi don ta shagaltar da jam’iyyun daga yin abun daya dace.
Sannan yace daga abin daya faru na korar Kwankwaso da gwamnan Kano da wani bangaren jam’iyyar NNPP yayi za’a fahimci cewa hakan wani abu ne da aka shirya. Saboda babu wata jam’iyyar da zata kori gwamna mai ci a cewar sa.