Wani matashi dan shekara 14 ya rasa ransa sannan wasu 21 suka ji manyan rauni sanadiyyar fashewar Gas din girki a unguwar Goron Dutse dake jihar Kano.
Lamarin ya faru a fitaccen Malamin Islama Marigayi Malam Isyaka Rabi’u, a jiya litinin, inda rahotanni suka bayyana cewa da misalin karfe 2:30, P.M fashewar Gas din ta afku a dakin girkin abinci.
Masu bayar da agajin gaggawa sunyi kokarin kai dauki wajen tare da kai wadanda suka jikkata zuwa asibiti don basu kulawa.
Rundunar yan sandan jihar Kano tace fashewar ta fara ƙone wasu sassan gidan kafin masu kashe gobara su kawo dauko.
Tuni an kai wadanda suka jikkata asibitocin Gamji, Murtala dana Orthopaedic.