Tsohon gwamnan jihar Sokoto Attahiru Bafarawa, ya musanta komawa jamiyyar SDP.
Jaridar Punch, ta rawaito cewa daya daga cikin hadiman Bafarawa daya nemi a sakaya sunan sa shine ya sanar da ita cewa batun komawar mai gidan nasa zuwa SDP da ake yadawa ba gaskiya bane.
:::Sojoji sun kashe yan bindiga 37 a Zamfara
A safiyar yau Talata ne aka samu wasu daga cikin kafafen yada labarai na shafukan sada zumunta sun wallafa labarin cewa Bafarawa, ya koma SDP.
Idan za’a iya tunawa a watannin baya tsohon gwamnan na Sokoto ya sanar da ficewa daga jam’iyyar PDP, sannan yace ya bar shiga sha’anin siyasa inda yace zai mayar da hankali wajen kawo cigaban rayuwar mutanen arewa.