Yan ta’adda sun kashe mutane 13, da kone kauyuka 7

0
72

Wasu bata gari da ake kyautata zaton yan ta’adda ne sun kashe mutane 13 da kone kauyuka 7, a jihar Kebbi.

Lamarin ya faru yayin da mayakan suka kai wani hari a kusa da kauyen Birnin dede, wanda ake zaton an kai harin don daukar fansa.

Maharan sun yi wannan barna a Karamar Hukumar Arewa a jiya Lahadi, biyo bayan kisan wani babban dan ta’adda mai suna Maigemu, da jami’an tsaro suka yi.

:::Gwamnatin tarayya ta roki Musulman Njeriya su sake zabar Tinubu

Wani mazaunin inda lamarin ya faru mai suna Malam Umar ya sanar da manema labarai cewa an kone kauyuka da dama sai dai yan ta’addan sun kasa samun damar kona wani kauye daya saboda jami’an tsaro sun kawo dauki, yana mai cewa suna neman taimako daga Allah akan wannan musifar hare-haren yan bindiga.

Gwamnan jihar Kebbi Nasir Idris, shine ya nemi a kara kokari wajen kashe yan ta’adddan dake hallaka mutanen jihar kuma haka ne yasa aka samu nasarar kisan maigemu.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here