NNPCL ya dena siyarwa matatar Dangote danyen man fetur

0
38

Ana fargabar samun tashin farashin man fetur, biyo bayan yadda kamfanin NNPCL ya yanke shawarar dena siyarwa matatar man fetur ta Dangote danyen mai da takardar Kudi ta Naira.

Jaridar The Cable, tace NNPCL ya dena siyarwa kowacce matatar cikin Najeriya danyen mai da Naira sai dai Dala, da ake ganin hakan zai sanya fetur yin tsada.

The cable, tace daukar matakin da NNPCL yayi zai sanya matatun mai na cikin gida su fara neman dalar Amurka da zasu rika siyo danyen man daga kasashen ketare, wanda hakan na daya daga cikin dalilan dake kawo tashin farashin man fetur a Najeriya, bisa hujjar cewa ana samun karancin takardun kudi na Dala.

Idan za’a iya tunawa a ranar 1 ga watan Oktoba na shekarar 2024, aka kaddamar da shirin siyar da danyen man fetur da takardar Kudi ta Naira kamar yadda shugaban kasa Tinubu ya bawa kamfanin NNPCL umarni da nufin É—aga darajar naira da kuma saukakawa matatun man fetur na Nigeria.

Bisa ka’ida an ce za’a dakatar da shirin siyar da danyen man da Naira a shekarar 2030, sai dai wasu manyan majiyoyi sunce NNPCL ya sanar da matatar Dangote da sauran matatun cikin gida cewa an dakatar da shirin a yanzu.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here