Malam Nasir El-Rufa’i ya koma jam’iyyar SDP

0
36

Tsohon gwamnan jihar Kaduna Malam Nasir El-Rufa’i, ya fice daga jam’iyyar APC tare da komawa SDP.

Jaridar Vanguard, ta rawaito cewa El-Rufa’i ne ya sanar da ficewar tasa daga APC cikin wani sakon daya wallafa a shafin sa na Facebook, a yau Litinin.

:::Jam’iyyar APC ta nemi a tsige gwamnan jiihar Rivers

Tsohon gwamnan yace tuni ya mika takardar ficewar tasa daga APC ga shugabancin jam’iyyar na mazabar sa, bayan kammala tattaunawa da magoya bayan sa kafin daukar matakin.

El-Rufai ya zargi shugabannin jam’iyyar APC da yin watsi da matsalolin cikin gida da kuma tauye tsarin dimokuradiyya.

Ya kuma ce a matsayin sa na mamba a jami’yyar SDP, zai jagoranci hadin kan jam’iyyun adawa don kalubalantar APC a zaben shekarar 2027, yana mai cewa APC tana daukar sa a matsayin wanda ba dan jam’iyyar ba duk da cewa yana daga cikin na gaba-gaba wajen kafa jam’iyyar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here