Gwamnatin tarayya ta roki Musulman Njeriya su sake zabar Tinubu

0
60

Ministan ayyuka David Umahi, ya roki al’ummar musulmi suyi addu’a sannan su sake zabar Tinubu a matsayin shugaban kasa karo na 2 a kakar zabe ta shekarar 2027.

Umahi, ya tabbatarwa da yan Najeriya cewa Tinubu yana da kyakkyawar manufar sanya yan kasa a cikin walwala da nishadi, yana mai cewa tun a yanzu an fara samun saukin tsadar rayuwar da ake ciki.

:::Malam Nasir El-Rufa’i ya koma jam’iyyar SDP

Ministan ya bayyana hakan a jiya lahadi lokacin da yake taya al’ummar musulmi yin buda bakin azumi a Abakaliki dake jihar Ebonyi.

Ya kara da cewa yan Najeriya ba zasu sake shiga kunci ba a lokacin mulkin Tinubu.

Umahi, ya kuma nemi duk lokacin da musulmai zasu yi addu’a su rika yiwa Tinubu don ya samu nasara a zabe mai zuwa.

Da yake nasa jawabi yayin shan ruwan shugaban musulman jihar Ebonyi Alhaji Danjuma Gambo, ya nuna farin cikin sa akan yadda ministan yake nunawa kowanne bangaren addini kauna.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here