Hukumar kula da albarkatun man fetur ta kasa NMDPRA ta bawa wasu kamfanoni 3 lasisin buɗe matatun man fetur a Najeriya.
NMDPRA ta sanar da hakan a jiya Juma’a cikin wata sanarwa data fitar a shafin ta na X, inda tace matatun zasu rika tace danyen man fetur da yawan sa yakai ganga dubu 140 a kowacce rana.
Hukumar NMDPRA tace matatar Eghudu, zata rika tace gangar mai mai dubu 100 a rana, sai matatar MB da zata rika tace gangar mai dubu 30 a rana, yayin da HIS zata tace ganga dubu 10 kowacce rana.
Shugaban hukumar NMDPRA Injiniya Farouk Ahmad, ne ya bayar da lasisin, wanda za’a samar da matatun a jihohin Edo, Abia, da Delta.