Tsagerun Neja Delta sun gargadi gwamnatin tarayya akan kar ta amince da hukuncin kotun koli da ya hana babban bankin kasa CBN turawa gwamnatin Rivers kudaden ta na wata-wata.
Tsagerun sun yi barazanar aikata ba daidai ba in har hakan ta tabbata.
Wasu daga cikin masana sunce rashin bawa Rivers kason kudin ta na wata-wata zai sanya a dena biyan tsagerun albashin su, kuma haka zai iya sawa su dauki makamai don cigaba da kawo matsala a wajen haƙar danyen man fetur.
Idan za’a iya tunawa kotun koli ce ta yanke hukuncin dena bawa gwamnatin Rivers kudi daga asusun gwamnatin tarayya akan rikicin dake tsakanin gwamnan jihar Siminalaya Fubara, da yan Majalisar Rivers masu goyon bayan ministan birnin tarayya Abuja Nyesom Wike, da hakan ya shafi kasafin kudin jihar.