An kama yan bindiga dauke da makamai a jihar Kano

0
111

Rundunar yan sandan jihar Kano ta kama wasu mutane 4 dauke da makamai wanda ake zaton yan ta’adda ne tare da samun kudade a wajen su lokacin da yan sanda ke yin rangadi a yankin Jarkuna dake karkashin kulawar jami’an ofishin yan sanda na Mariri.

A ranar 6 ga watan Maris aka kama mutanen da misalin karfe 4 na yamma.

Wadanda aka kama sun hadar da Shukurana Salihu, mai shekaru 25, sai Rabi’u Dahiru, mai shekaru 35, da Ya’u Idris, mai shekaru 30 dukkanin su daga jihar Katsina, sai Muktar Sani,  mazaunin unguwar Yandodo dake Hotoro, a jihar Kano.

Makaman da aka samu a wajen su sun hadar da bindiga hadin gida guda 3, sai adda guda biyu, da kunshin alburusai 12, wuka guda biyu, wayar salula 4, da katin shaidar zama É—an Bijilanti.

A wani cigaban rundunar yan sandan jihar Kano ta sanar da kama wasu barayin ababen hawa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here